Daga Mustapha Abdullahi
Wasu manoman shinkafa a Najeriya sun bayyana damuwarsu kan yadda karuwar shigo da shinkafa daga kasashen waje ke durkusar da harkar noma a cikin gida.
A tattaunawa da suka yi da kamfanin dillancin labarai na kasa a Lagos, manoman sun ce yawan shigo da shinkafa ya karu tun bayan sassaucin haraji da gwamnatin tarayya ta bayar a shekarar 2024.
Shugaban riko na kungiyar manoma ta kasa, Mista Sakin Agbayewa, ya ce wannan mataki ya jefa manoma cikin matsin lamba, inda ya kara da cewa sauyin yanayi da tsadar taki da sauran kayan noma na kara dagula harkar noman.
Karanta:Stakeholders Unveil Kubau Consultative Forum, Advocate Greater Devt
Ya bayyana cewa shinkafar da ake shigowa da ita tana zuwa da farashi mai rahusa fiye da ta gida, lamarin da ke sa manoma cikin asara tare da rage musu karfin gwiwar ci gaba da noma.
Shi ma shugaban kungiyar manoman shinkafa na jihar Lagos, Mista Raphael Hunsa, ya bukaci gwamnati ta kara tallafawa manoman gida, yana mai cewa yawancinsu na fuskantar matsaloli wajen samun riba saboda tsadar kayan aiki da rashin ingantaccen yanayin kasuwanci.
A bangaren masu sayar da shinkafa, wata ‘yar kasuwa a Agege, Tolu Ajiboye, ta ce farashin shinkafa ya ragu sakamakon yawaitar wacce ake shigowa da ita daga waje. Ta ce buhun kilo 50 da ake sayarwa sama da naira dubu 60 a baya, yanzu ana sayar da shi tsakanin naira dubu 51 zuwa 55.
Masu ruwa da tsaki sun yi gargadi cewa idan ba a dauki matakan tallafawa manoman gida ba, harkar noman shinkafa a Najeriya na iya kara tabarbarewa.
Recent:VP Shettima Leads Speaker Abbas, Others To Wedding Of Zulum’s Children
