Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Majalisar Kasa Kan sana’o’i da fasahar kere-kere na kwararru NCS ta yabawa Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, bisa nasarar kaddamarwa da kafa Majalisar jiha kan Sana’o’i da kere-kere ta Jihar Kaduna a zamanta na baya-bayan nan.
A wata wasika da ke dauke da sakon yabon, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa majalisar ta yaba da jagorancin gwamnan wajen jagorantar majalisar jihar, matakin da ya dace da manufar Sabonta fata wato “Renewed Hope Agenda” tare da kafa abin koyi ga sauran jihohi.
Ya ce, “Ta hanyar samar da tsari na musamman domin bunkasa kwarewa, Jihar Kaduna ta nuna jajircewa wajen rage gibin rashin aikin yi da kuma inganta ci gaban jarin dan Adam daidai da manufofin kasa.”
Karanta:An kashe Birgediya Janar Oseni Braimah a harin Boko Haram a Borno.
Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa kafa Majalisar Kwararru ta Kaduna shaida ce ta hangen nesa na gwamnatin Uba Sani wajen samar da ci gaban tattalin arziki mai hade.
Ya kuma bayyana cewa NCS na kallon tsarin Kaduna a matsayin muhimmin misali na dabarar daga kasa zuwa sama wajen koyar da sana’o’i, wanda ke taimakawa wajen kai shirye-shiryen horaswa na fasaha da sana’o’i har zuwa matakin kasa.
Yayin da ya bukaci gwamnan da ya ci gaba da wannan kokari, Shettima ya ce majalisar na fatan kara hada kai tsakanin sakatariyar kasa da majalisar jihar domin daidaita ka’idoji da fadada tasirin shirin.
A baya dai, Gwamna Uba Sani ya fadada ilimin fasaha da koyon sana’o’i ta hanyar kafa cibiyoyi uku na zamani na Kaduna State Institute of Vocational Training and Skills Development (KIVTSD).
Cibiyoyin uku da ke Soba, Rigachikun da Samarun Kataf a yankunan sanatoci na 1, 2 da 3, ana sa ran za su rika samar da kwararrun masu sana’a 12,000 a kowace shekara.
Masu koyon sana’o’in da suka hada da walda, hada aluminium, dinkin zamani, girka na’urorin hasken rana da sauransu, za a ba su takardun shaida bayan kammala horo.
Gwamnatin jihar Kaduna na kuma hada gwiwa da National Board for Technical Education (NBTE) domin tabbatar da ingantaccen tantancewar kwasa-kwasan.
Haka kuma, gwamnan na shirin gyara kasuwar Panteka mai dauke da kusan masu sana’a 38,000, domin mayar da ita cibiyar masana’antu, musamman a fannoni kamar walda, aikin katako da gini.
