Rikicin cikin gida na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kara tsananta, yayin da gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya nuna yiwuwar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa ta sirri da wata tawaga ta ADC karkashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal, wadda ta gudana a Fadar Shugaban Kasa da ke Bauchi.
A cewarsa, duk da kokarin da aka yi na sasanta rikice-rikicen cikin gida na PDP a matakin kasa da na jiha, har yanzu ba a samu wani ci gaba mai ma’ana ba.
Ya ce an kafa kwamitoci biyu domin tantance makomar siyasarsu, daya a Abuja a matakin kasa, da kuma wani a Bauchi, domin duba zabin da ke akwai har da yiwuwar komawa wasu jam’iyyu.
Karanta:An samu hauhawar farashin man fetur mafi girma cikin shekaru hudu a Amurka
Gwamna Bala Mohammed ya kara da cewa ci gaba da zama a cikin yanayin siyasa inda ba a maraba da su ba, ba zai yiwu ba, yana mai jaddada bukatar samun mafita a karkashin wata jam’iyyar adawa mai karfi.
Ya bayyana jam’iyyar ADC a matsayin wadda suke karkata a kai, sai dai ya ce har yanzu ana ci gaba da tuntuba da tattaunawa domin tabbatar da daukar mataki mai kyau.
Tun da fari, shugaban tawagar ADC, Babachir David Lawal, ya ce ziyarar tasu ta biyo bayan umarnin shugaban jam’iyyar na kasa, domin gayyatar gwamnan ya shiga ADC gabanin zabukan shekarar 2027.
Ya bayyana gwamnan a matsayin jarumin dan siyasa wanda shigarsa jam’iyyar zai kara mata karfi a zabuka masu zuwa.
Haka kuma ya jaddada bukatar hadin kan jam’iyyun adawa, yana mai gargadin cewa rashin hada kai na iya haifar da mummunan sakamako ga makomar Najeriya.
Wannan ganawa na zuwa ne kwanaki kadan bayan gwamnan ya kira taron masu ruwa da tsaki na PDP a Bauchi, da nufin warware sabanin cikin gida da kuma karfafa hadin kai a jam’iyyar.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa wannan sabon ci gaba na iya sauya yanayin siyasa a Jihar Bauchi da ma kasa baki daya, yayin da ake kara tunkarar zabukan shekarar 2027.
Recent:DA DUMI-DUMI: ‘Yan majalisar wakilan Nijeriya 8 daga Kano sun fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC
