Daga Mustapha Abdullahi
Daraktan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Masar, Ibrahim Hassan ya gargadi Mohamed Salah da ka da ya koma Gasar Major League Soccer (MLS) bayan ya bar Liverpool a ƙarshen kakar wasa, yana mai cewa hakan zai iya sa shahararsa ta daƙushe.
Salah mai shekaru 33, har yanzu bai yanke shawara ba game da matakinsa na gaba bayan ya kammala zaman shekaru tara masu nasara a Liverpool, inda ya lashe kofunan Premier League biyu da kuma Champions League.
karanta:DA DUMI-DUMI: ‘Yan majalisar wakilan Nijeriya 8 daga Kano sun fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC
Kwamishinan MLS, Don Garber ya ce zai yi farin ciki idan ya ga Salah ya shiga gasar, duk da cewa ba a tabbatar ko wasu ƙungiyoyin MLS za su yi ƙoƙarin ɗaukarsa ba.
“Ni da kaina, zan fi son ya ci gaba da zama a Turai,” in ji Hassan yayin wata hira da On Sports. “Na ji labarin tayin daga Paris Saint-Germain, Bayern Munich da kuma wasu ƙungiyoyi a gasar Italiya.” kamar yadda TRT Afrika Hausa ta rawaito
