Daga Mustapha Abdullahi
Moses Simon da Akor Adams ne suka jefa wa Super Eagles ƙwallo a raga.
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles, ta doke ƙasar Iran da ci 2 da 1 da wasan sada zumunta da suka buga a ranar Juma’a.
Ƙasashen biyu sun kara da juna a filin wasa na Mardan Sport Complex da ke yankin Antalya na ƙasar Turkiyya.
Ɗan wasan gaban Super Eagles, Moses Simon ne ya fara jefa ƙwallo a raga a minti 6 da fara wasan.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Akor Adams ya jefa wa Najeriya ƙwallo ta biyu a raga a minti ma 51.
Shi kuma ɗan wasan gaban ƙasar Iran Mehdi Taremi ya jefa wa ƙasarsa ƙwallo a raga.
Karanta:An fara gangamin tara wa Tinubu magoya baya miliyan 150 -Benjamin Kalu
’Yan wasan Super Eagles, Samuel Chekwueze da Ademola Lookman ne suka taimaka wajen jefa wa Super Eagles ƙwallaye biyu a raga.
Fitaccen ɗan wasan gaban Super Eagles, Victor Osimhen bai samu buga wasan ba sakamakon raunin da ya samu a hannunsa a wasan da Galatasaray ta yi da Liverpool a Gasar Zakarun Turai.
Recent:Gwamnan Nasarawa A.A Sule ya musanta haduwa da Atiku a Saudiyya
