AISHA HUMAIRA TA BUKACI BAANA YA JANYE KALAMANSA AKANTA DA MIJINTA HAR SAUBIYU AMMA YAKI
Rikicin da ya kunno kai tsakanin shahararriyar mawakiya Aisha Humaira da fitaccen jarumin taƙaddama Baana na cigaba da daukar zafi, bayan da rahotanni suka tabbatar da cewa Aisha ta kai korafi gaban hukumomi domin kare mutuncinta.
Majiyoyi sun bayyana cewa an kira Baana ya janye kalamansa sau biyu, amma yayi koboho, lamarin da ya jefa al’amuran cikin sabon salo.
A cewar wasu majihoyi, wutar rikicin yana kara konnowane sakamakon shigar da ƙara a hukumance, domin tilasta Baana ya gabatar da hujjojin da yake ikirarin yana da su a bainar jama’a.
Rahotanni sun tabbatar da cewa DSS na da kwafin petition ɗin, kuma ana shirin gurfanar da lamarin a gaban kotu domin gudanar da bincike akan lamarin.
Rikicin yasoma tasowane a wani faifan video da baana ya wallafa a shafin tiktok yake yin bayani kamar haka.
“Kuduba wannan yarinyar rare kaji tsoron Allah saidai kusa ayita kawo muku tikatikan yan mata da zawarawa suzo suta kada duwawu da no nonuwa Amma ka kasa biyanmu bashin da muke binka,haka kake daukan matarka humaira kake kaita cikin maza suna tattaba ta, kuduba yadda Tinubu ya mika mata hanu”
Wadanan kalamai na baana sune suka harzuka Aisha Humaira har tafita ta nuna rashin jin dadinta gameda yadda baana yayi mata, har tanemeshi da yafito yajanye kalamasa marasa dadi akanta.
Kalaman Aisha Humaira “Nasan Doka Nasan Inda Hukuma Suke
Sannan nasan banfi karfin ko wace doka ba
Ina Neman Hakki Ne a wajen wanda ya zalinceni Kuma lya Hakki na kadai nake nema,kamar yadda nasan dukkan laifi yana nan a rubuce a cikin kundin doka”
Ana sa ran nanda makonnin kadan Baana zai gurfana a gaban kuliya domin tabbatar da gaskiya da ƙarya, tare da nunawa ko Baana zai iya tabbatar da abinda yake faɗi—ko kuma lokaci zai yi masa kaca-kaca.
