Daga Mustapha Abdullahi
Rundunar ’yansanda a jihar Kano na neman dangin wani yaro ɗan shekara 16 mai suna Alex Ansol daga ƙasar Spain, wanda aka tsinta yana yawo a ƙauyen Dadin Kowa da ke ƙaramar hukumar Doguwa.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Ya ce Alex ya iso Najeriya tare da wasu ’yan uwansa huɗu a ranar 30 ga Maris ta filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Abuja. Sai dai ya ɓace daga cikinsu ne a kan hanyar Jos zuwa Saminaka yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kano domin ziyartar mahaifinsa, Ansol Fan.
A cewarsa, yaron yana magana da Turanci, siriri ne.
Karanta:Sojoji sun kashe ’yan bindiga 65 a Zamfara, ciki har da ɗan shugaban ‘yan ta’adda
Haka kuma ya bayar da adireshinsa a matsayin “Barsa Rub, Opposite 46 Stadium, Spain.”
Rundunar ’yansanda ta buƙaci duk wanda ke da bayani game da iyalansa da ya tuntube su ta lambar waya 07038363421 ko kuma ofishin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar a Kano.
Recent:Likitoci masu neman kwarewa sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani
