Daga Sani Adamu Hassan
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya jaddada cewa ba zai bar jam’iyyar PDP ba duk da ƙalubalen da take fuskanta a halin yanzu kamar yadda daily post ta rawaito.
Lamido ya bayyana PDP a matsayin gida a gare shi, yana mai cewa bai dace ba ɗan siyasa ya bar jam’iyya saboda tana cikin matsala.
A cewarsa, irin wannan mataki ba ya nuna kishin jam’iyya ko jajircewa wajen gina dimokuraɗiyya.
karanta:Likitoci masu neman kwarewa sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani
Ya kuma soki wasu ‘yan siyasa da suka fice daga PDP suna komawa ƙananan jam’iyyu kamar ADCz yana cewa hakan na iya janyo rauni ga tsarin siyasar ƙasar.
Lamido ya yi kira ga dukkan mambobin PDP da su haɗa kai domin gyara jam’iyyar daga ciki, maimakon barinta, domin ta sake samun ƙarfi kafin babban zaɓen shekarar 2027.
Recent:’Yansanda a Kano na neman iyayen wani yaro da ya ɓata bayan sun zo daga ƙasar Spain
