Daga Mustapha Abdullahi
Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da kashe aƙalla ’yan bindiga 65, ciki har da Kachalla Iliya Sarki, ɗan fitaccen shugaban ‘yan ta’adda Ado Allero, a wani gagarumin samame da aka kai a ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da farmakin ne ta hanyar haɗin gwiwar hare-haren ƙasa da sama, inda aka kai wa ’yan bindigar hari a ƙauyen Munhaye da ke bayan Kunchin Kalgo. An ce harin ya yi mummunar illa ga ƙungiyoyin ’yan ta’adda da ke haddasa rikice-rikice a jihohin Zamfara, Katsina da wasu sassan Kano.
Wata majiya ta tsaro ta ce an fara fafatawar ne da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Asabar, inda aka shafe sama da sa’o’i bakwai ana artabu mai tsanani tsakanin sojoji da ’yan bindigar, tare da tallafin hare-haren jiragen sama da suka lalata sansanonin su.
karanta:ADC Na Firgita Wasu, Zaben 2027 Zai Zama Mai Zafi — Aisha Yesufu
An kuma rawaito cewa Ado Allero ya tura mayaka da dama domin tunkarar sojojin, inda aka ce sun yi amfani da kimanin babura 300 daga yankin Yan Wari domin ƙoƙarin dakile farmakin. Haka kuma an turo ƙarin mayaka daga sansanin Dankarami Gwaska domin taimaka musu.
Daga cikin waɗanda aka kashe har da wasu manyan shugabannin ’yan bindiga biyu, Dogo Sule da Iliya Mai Rasha. Rahotanni sun nuna cewa Mai Rasha ne ya karɓi jagoranci bayan kashe wani kwamanda mai suna Alti a watan da ya gabata.
Sai dai a yayin artabun, ’yan sa-kai bakwai da ke taimaka wa sojojin sun rasa rayukansu.
Bayan kammala farmakin, an ce Ado Allero ya tsere, kuma yanzu yana ɓoye a garin Yankuzu, yayin da sojoji ke ci gaba da farautarsa.
