Daga Mustapha Abdullahi
Rikicin cikin gida na jam’iyyar APC a jihar Bauchi na ci gaba da ƙamari, yayin da ‘yan takarar gwamna ke kasa cimma matsaya kan wanda zai zama ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa duk da yunkurin samar da maslaha, ‘yan takarar sun kasa amincewa da juna, lamarin da ya haifar da tsaiko a shirye-shiryen jam’iyyar a jihar.
Karanta:Sule Lamido ya ce ba zai bar PDP ba duk da matsalolinta
Daga cikin masu neman takarar akwai Ministan Lafiya, Muhammad Ali Pate, wanda rahotanni ke cewa bai janye daga burinsa ba.
Haka kuma akwai Yusuf Maitama Tuggar wanda ya yi murabus daga mukaminsa domin neman tikitin gwamna, baya ga sauran ‘yan takara kamar Shehu Buba da Bala Wunti.
Recent:Ƴan ta’adda sun kai hari kan cocin Kaduna, sun kashe mutane bakwai, sun sace wasu.
