Daga Mustapha Abdullahi
Jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya reshen jihar Kano za ta gudanar da taron zaben shugabanninta a matakin jiha a yau Asabar a jihar.
Sakataren yaɗa labarai na riko na jam’iyyar, Engr Ibrahim Karaye ne ya baiyana haka a wata sanarwa, inda ya ce za a gudanar da taron ne domin zaɓen sabbin shugabanni na jiha.
karanta:Najeriya ta doke Iran da ci 2 a wasan sada zumunta
Ya ce za a yi taron a.ofishin jam’iyyar da ke gidan Lugard a Kano, da misalin ƙarfe 1 na rana, inda ake sa ran jagororin jam’iyyar za su halarci taron don zaɓen sabbin shugabannin.
Hakan ne zuwa ne yayin da jita-jita ke kara ƙarfi cewa jagoran jam’iyyar na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai sauya sheƙa zuwa jam’iyyar adawa ta ADC.
Recent:An Nemi Tinubu Ya Taka Wa Gwamna Bago Birki A Kan Cin Zarafin Kafafen Yada Labaru.
