Daga Mustapha Abdullahi
Kasashen Nijar da Türkiye sun rattaba hannu kan yarjejeniyar horas da sojoji domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.
Karanta:Malam Abduljabbar da aka yanke wa hukuncin kisa ya nemi a mayar da shi gidan yari na Kano daga Kuje
Wannan ya biyo bayan wata ganawa da jami’an ƙasashen biyu suka yi a ranar Talata, karkashin jagorancin Ministan tsaron Turkiyya, Yaşar Güler, da kuma Ministan tsaron Nijar, Salifou Mody.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Turkiyya ta fitar, ta ce ministocin biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar samar da horo a tsakanin gwamnatocin ƙasashen biyu, domin inganta ƙwarewar sojojin Nijar da ƙarfafa tsaro a yankin.
Recent:Atiku ga Tinubu: Raba shinkafa da taliya ba zai cece ka ba a zaɓen 2027
