Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Akalla mutane 11 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon wani rikicin ƙabilanci da ya ɓarke a Jihar Nasarawa, inda fiye da gidaje 50 suka lalace sakamakon tashin hankalin.
Rikicin ya janyo asarar dukiyoyi da kuma raba mutane da muhallansu, bayan da aka kona gidaje da kadarori a yayin harin.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga saɓani tsakanin wasu ƙungiyoyi, wanda daga bisani ya rikide zuwa mummunan artabu mai janyo asarar rayuka. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa rikicin ya bazu cikin sauri, lamarin da ya haddasa ɓarna mai yawa da kuma asarar rayuka a yankunan da abin ya shafa.
Tuni jami’an tsaro suka isa wurin domin dawo da zaman lafiya, yayin da hukumomi ke kokarin tantance ɓarnar da aka yi tare da daukar matakan hana sake faruwar irin wannan rikici.
Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomi da su gaggauta daukar matakan da suka dace domin kawo karshen rikice-rikicen da ke yawan faruwa a yankin.
Recent:Kada a bar jihar Plateau ta ci gaba da zama shalkwatar zubar da jinin al’umma – Shugaban APC na ƙasa
