Kwamishinan ’yan sandan ya yi Allah-wadai da wannan ɗanyen aiki, yana mai cewa abu ne mai tayar da hankali da rashin imani.
Rundunar ’yan sanda ta Jihar Jigawa ta fara bincike kan wani matashi mai shekara 27 da ake zargin ya banka wa mahaifinsa wuta a Karamar Hukumar Kazaure, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.
lamarin ya auku ne da asubahin ranar 1 ga watan Afrilu, 2026, a unguwar Lokon Malamai da ke hanyar rukunin gidaje na Magama a cikin garin Kazaure.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 6:30 na safe cewa an banka wa wani mutum wuta.
Ya ce nan take jami’ai suka garzaya wurin da abin ya faru, inda suka ɗauki wanda abin ya shafa zuwa asibiti domin ceto rayuwarsa.
Binciken farko ya nuna cewa kimanin mintuna 30 kafin samun rahoton, wanda ake zargi ya zuba wani abu mai saurin kamawa da wuta, wanda ake kyautata zaton fetur ne, a jikin mahaifin nasa sannan ya cinna masa wuta.
Daga bisani jami’an tsaro sun kama wanda ake zargin, mai suna Kabiru Nuhu, wanda rahotanni suka bayyana cewa shi ne ɗan mamacin.
’Yan sanda sun ce an same shi da raunukan ƙunar wuta a goshinsa da hannuwansa da kuma yatsun ƙafafunsa, lamarin da ya ƙara tabbatar da zargin da ake yi masa.
Karanta:An kama ’yan Najeriya uku a India kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
Tun da farko dai an kai mahaifin mai kimanin shekaru 60 wani babban asibiti domin ƙarin kulawa, amma daga bisani ya rasu yana karɓar magani.
A halin yanzu, wanda ake zargin yana hannun ’yan sanda, kuma za a miƙa shi zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar da ke Dutse domin ci gaba da bincike gabanin gurfanar da shi a gaban kotu.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Haruna Alaba Yahaya, ya yi Allah-wadai da wannan ɗanyen aiki, yana mai cewa abu ne mai tayar da hankali da rashin imani.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su riƙa neman hanyoyin sulhu idan saɓani ya taso, maimakon ɗaukar doka a hannu, tare da gaggauta kai rahoton rikice-rikice ga hukumomin tsaro.
Hukumomi sun buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu yayin da ake ci gaba da bincike, tare da alƙawarin sanar da su duk wani sabon bayani.
Recent:ADC Na Firgita Wasu, Zaben 2027 Zai Zama Mai Zafi — Aisha Yesufu
