Daga Mustapha Abdullahi
Wani malami a sashen gudanar da harkokin jama’a na Kwalejin fasaha ta jihar Kogi, Mista Anslem Ojodomo, ya rasu yayin da yake koyarwa a cikin aji.
Shugaban kwalejin, Farfesa Salihu Avidime, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana mutuwar a matsayin babban abin jimami ga al’umma da iyalansa.
Rahotanni sun nuna cewa malamin ya fadi ne a lokacin da yake koyar da dalibai, inda aka garzaya da shi asibiti amma aka tabbatar da rasuwarsa.
Lamarin ya janyo fargaba a tsakanin dalibai da ma’aikata, musamman ganin cewa wannan na zuwa ne bayan mutuwar wani malami a kwalejin cikin kankanin lokaci.
Marigayin ya kasance kwararren malami mai jajircewa, wanda ya yi aiki a kwalejin tun shekarar 2021, tare da bayar da gudunmawa a fannoni daban-daban.
Kwalejin ta jajanta wa iyalansa tare da addu’ar Allah ya jikansa.
Recent:Dubban Amurkawa za su yi zanga-zangar adawa da mulkin Trump
