Daga Mustapha Abdullahi
Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara, malamin addinin Musulunci a jihar Kano da aka yanke wa hukuncin kisa bisa zargin ɓatanci ga addini, ya sake shigar da ƙorafi a kotu, yana neman a dawo da shi gidan Yarin Kurmawa da ke Kano daga na Kuje da ke Abuja.
A cikin takardar korafin da aka miƙa wa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Kano mai ɗauke da kwanan watan 3 ga Afrilu, 2026, Kabara ya ce sauya masa wuri.zuwa Abuja ya hana shi samun muhimman takardun shari’arsa da yake buƙata domin ɗaukaka ƙara.
Ya bayyana cewa takardun, waɗanda suka ƙunshi fiye da shafuka 5,000 na bayanan shari’a da hujjojin lauya, an bar su ne a gidan yarin Kurmawa lokacin da aka sauya masa wuri a ranar 14 ga Oktoba, 2025.
Karanta:Ƙungiyar ASUU ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani a Jami’ar Jos
Kabara, wanda ya dage cewa zai kare kansa da kansa a wannan ɗaukaka ƙara, ya jingina buƙatarsa da Sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulkin ƙasa na 1999.
A tuna cewa tun a ranar 15 ga Disamba, 2022, wata kotu ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Ibrahim Sarki-Yola ta yanke wa Malam Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi a kan dukkan tuhume-tuhume huɗu da gwamnatin jihar Kano ta shigar a kansa.
Recent:Mazauna ƙauye sun hallaka ’yan fashi uku a Sokoto bayan artabu mai tsanani.
