Daga Mustapha Abdullahi
Ƙungiyar likitoci masu neman kwarewa ta sanar da shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a faɗin Najeriya daga ranar 7 ga Afrilu, 2026 kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Sakataren ƙungiyar, Shuaibu Ibrahim, ya ce matakin ya biyo bayan dakatar da aiwatar da sabon tsarin alawus na ƙwararru (PAT) da gwamnatin tarayya ta yi.
Karanta:Matashi ya cinna wa mahaifinsa wuta a Jigawa
Ƙungiyar ta bayyana matakin a matsayin karya yarjejeniya, tana mai buƙatar gwamnati ta janye shi tare da biyan dukkan haƙƙoƙin likitoci.
NARD ta kuma buƙaci mambobinta su kasance masu haɗin kai har sai an warware matsalar.
Recent:Sojoji sun kashe ’yan bindiga 65 a Zamfara, ciki har da ɗan shugaban ‘yan ta’adda
