Daga Mustapha Abdullahi
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya buƙaci a samar da mafita mai ɗorewa kan hare-haren kisan gilla da ke yawaita a Jihar Plateau kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

Yilwatda ya bayyana haka ne a Jos yayin ziyarar jajantawa da Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya kai wa iyalan waɗanda aka kashe a harin Angwan Rukuba da ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 28.
Ya yabawa Tinubu kan ziyarar, yana mai cewa hakan alama ce ta shugabanci mai tausayi da haɗin kai na ƙasa. Haka kuma ya la’anci harin, yana kiran sa rashin imani da kuma barazana ga zaman lafiya a jihar.
Ya jaddada cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa tare da haɗin gwiwar kowa domin dakile hare-haren, yana mai cewa masu aikata laifukan ba baƙi ba ne, sai dai wasu daga cikin al’umma.
Yilwatda ya kuma buƙaci jami’an tsaro su sabunta dabarunsu ta hanyar amfani da fasahohin zamani kamar na’urorin leƙen asiri, jirage marasa matuƙa da tsarin
