Daga Mustapha Abdullahi
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana shirin hada matasa, tsofaffin sojoji da sauran fararen hula cikin ayyukan kawar da ababen fashewa domin dakile barazanar na’urorin fashewa na IEDs da nakiyoyin kasa.
Ministan Tsaro, Christopher Musa ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki kan ayyukan kawar da nakiyoyi da aka gudanar a Abuja.
Ta bakin sakataren din-din-din na ma’aikatar tsaro, Richard Pheelangwah, ministan ya ce wannan shiri zai taimaka wajen karfafa kokarin da ake yi na rage hadarin nakiyoyi da ake dasawa musamman a yankunan da ke fama da rikicin ‘yan tada kayar baya.
Karanta:An gurfanar da ma’aikacin NYSC a kotu bisa zargin bai wa budurwa maganin zubar da ciki har ta mutu
Ya ce za a kafa kungiyoyin fararen hula masu aikin kwance nakiyoyi, wadanda za su kunshi tsofaffin injiniyoyin soja, kwararrun jami’an tsaro, likitoci da kuma matasa da aka horar.
Recent:Albarka Radio Demands Justice Over Alleged Assault On Reporter, Seeks Suspension Of DPO
