Daga Mustapha Abdullahi
Wannan buƙatar na daga cikin abubuwan da aka tattauna a zaman majalisar tarayyar ƙasar a ranar 31 ga watan Maris, 2026 a lokacin da aka karɓi rahoton kasafin kuɗin 2026.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, gwamnatin ƙasar ta sanya wannan buƙatar a cikin kasafin kuɗin, inda suke cikin rukunin kuɗaɗen da ake kashewa na ko ta kwana, amma ba a alaƙanta su da ko wace ma’aikata ko hukuma ba.
karanta:Babu hannun Shugaba Tinubu a rikicin jam’iyyar ADC – Cewar Bayo Onanuga
Masana tattalin arziki da shari’a sun bayyana cewa irin wannan tanadi yana nuna cewa gwamnati na tsammanin matsin lamba daga shari’o’in da suka shafi zaɓe, ciki har da sasanta rikice-rikice da sauran tsarin gudanarwa da ke biyo bayan zaɓuka.
A shekarar 2027 ne za a gudanar da manyan zaɓukan ƙasar na shugaban ƙasa, da ƴanmajalisa da gwamnoni a wasu jihohin ƙasar saboda ƙarewar wa’adin mulkinsu.
Recent:Majalisar dokokin Kano ta jingine tuhumar da take wa tsohon mataimakin gwamna Aminu Abdussalam.
