Daga Mustapha Abdullahi
Ana sa ran miliyoyin jama’a za su fito zanga-zanga a faɗin ƙasar Amurka a yau Asabar domin nuna adawa da Shugaban ƙasar, Donald Trump, kan manufofinsa da salon mulkinsa.
Rahotanni sun nuna cewa wannan zanga-zangar na ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna “No Kings”, wadda ke jagorantar adawa da gwamnatin Trump tun bayan fara wa’adinsa na biyu a watan Janairu 2025.
Karanta:An Nemi Tinubu Ya Taka Wa Gwamna Bago Birki A Kan Cin Zarafin Kafafen Yada Labaru.
An ce wannan shi ne karo na uku cikin ƙasa da shekara guda da ake shirya irin wannan zanga-zanga, inda jama’a ke ƙara nuna fushinsu kan wasu manufofi ciki har da yaƙin da Amurka ke yi da Iran.
