Daga Mustapha Abdullahi
An bayyana sauyin sheƙar tasu ne a zaman majalisa na ranar Talata, wanda kakakin majalisar, Tajudeen Abbas, ya jagoranta.
Jaridar Punch ta ambato wasikunsu da aka karanta a zauren majalisar, ‘yan majalisar sun danganta matakin nasu da rikicin cikin gida da ke addabar NNPP.
Karanta:Kasashen duniya 10 ne suka amince da jakadun Tinubu, yayin da sauran ke jiran tsammani
Taron sauyin shekar ya samu halartar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin; da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da sauransu.
Recent:An samu hauhawar farashin man fetur mafi girma cikin shekaru hudu a Amurka
