Daga Sani Adamu Hassan
Jagoran jam’iyyar NNPP na Nijeriya, wanda kuma ya yi wa jam’iyyar takarar shugaban kasa a zaben 2023 Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fita daga jam’iyyar ya koma jam’iyyar hamayya ta ADC, kamar yadda wani makusancinsa ya wallafa a shafin Facebook ranar Asabar da daddare.
Karanta:Bauchi Moves To Establish Mining Institute, Seeks Partnership With Jos-Based Institute
Sakataren Kwankwasiyya Movement Dakta Yusuf Kofar Mata ya bayyana cewa tsohon gwamnan na Kano zai yi rijista a sabuwar jam’iyyar ranar Litinin mai zuwa, don haka ake gayyatar magoya bayansa su halarta.
TRT Afrika Hausa ta rawaito cewa kawo yanzu dai ba a bayyana dalilan Kwankwaso na fita daga NNPP ba, sai dai a baya bayan nan jam’iyyar tana fama da rikice-rikece na shugabanci abin da ya kai ga shari’a.
Recent:COAS To Troops: Apply Training Effectively, Stay Disciplined
