Daga Sani Adamu Hassan
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa raba buhunan shinkafa da taliya da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yake rabawa ba zai ce shi ba tsira a zaɓen shekarar 2027.
Atiku ya ce a halin yanzu, dimokuraɗiyyar Najeriya na fuskantar barazana, inda ya zargi gwamnatin Tinubu da yunƙurin murƙushe ƴan adawa.
Karanta:Mazauna ƙauye sun hallaka ’yan fashi uku a Sokoto bayan artabu mai tsanani.
Daily Trust ta ruwaito cewa a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata a Abuja ta hannun Babban Mataimaki na Musamman ga Atiku kan Harkokin Sadarwa, Phrank Shaibu, Atiku ya ce abin da ke faruwa a yanzu ba na bazata ba ne, illar ganganci ne.
Ya ce duk da cewa fiye da gwamnonin jihohi 30 na kusa da jam’iyyar APC mai mulki, ya kamata a ce gwamnati ta nuna kwarin gwiwa, buɗaɗɗen siyasa da kuma shirinta na fuskantar adawa ta gaskiya a zaɓe.
Sai dai, a cewarsa, abin da ‘yan Najeriya ke gani akasin haka ne, domin akwai alamun da ke nuna tsoron adawa mai ƙarfi, tsoron gasa ta gaskiya, da kuma tsoron ƙuri’ar al’umma.
Recent:Malam Abduljabbar da aka yanke wa hukuncin kisa ya nemi a mayar da shi gidan yari na Kano daga Kuje
