Daga Mustapha Abdullahi
Hukumomin tsaro a ƙasar India sun kama wasu ’yan Najeriya uku a bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi, ciki har da hodar iblis (cocaine) da kuma MDMA.
A birnin Hyderabad, jami’an tsaro sun cafke wata ’yar Najeriya bayan sun samu sahihan bayanan sirri cewa ta iso daga Mumbai domin sayar da miyagun ƙwayoyi. An same ta da gram 7.5 na hodar iblis, inda ake zargin ta sayo kayan a Mumbai kan farashi mai rahusa, tana shirin sayar da su a farashi mafi tsada.
A wani samame daban a New Delhi, jami’ai sun kama wani ɗan Najeriya mai suna John Chibuike tare da kilo ɗaya na hodar iblis a gidansa. Rahotanni sun nuna cewa ana zargin sa da jagorantar wata babbar ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi, tare da cewa yana da tarihin aikata irin wannan laifi tun daga shekarar 2022.
karanta:Kada a bar jihar Plateau ta ci gaba da zama shalkwatar zubar da jinin al’umma – Shugaban APC na ƙasa
Haka kuma, a birnin Bengaluru, jami’an tsaro sun kama wani ɗan Najeriya daban da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi nau’in MDMA mai yawa.
Hukumomin India sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran mutanen da ke da hannu a wannan haramtacciyar sana’a, tare da ɗaukar matakan da suka dace don rusa hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar.
Recent:Mutane 11 sun mutu, gidaje 52 sun kone a sabon rikicin ƙabilanci a Jihar Nasarawa
