Daga Mustapha Abdullahi
Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya bukaci kungiyar magoya bayan Tinubu ta Renewed Hope Partners ta tara akalla mutane miliyan 150 domin goyon bayan tazarcen Bola Tinubu a 2027.
Kalu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin karbar bakuncin tawagar kungiyar daga jihohin Edo, Ekiti da Katsina, inda ya jaddada cewa manufar kungiyar ita ce yada ayyukan gwamnati da karfafa dimokuradiyya.
Karanta:Bauchi Govt dissolves health college management, sets up interim team
Ya ce wajibi ne kungiyar ta yada manufofin “Renewed Hope Agenda” a ko’ina cikin al’umma, ciki har da kasuwanni, masallatai, coci-coci, tashoshin mota da kuma jami’o’i.
Jaridar Daily Nigerian ta ambato Kalu ya kara da cewa suna shirin kafa rassa a dukkan jami’o’i da kananan hukumomi domin tabbatar da cewa sakon gwamnati ya isa ga kowane dan kasa.
Recent:Advocacy Visit Reveals Gaps In Bauchi Health Facilities, Stakeholders Seek Urgent Action
