’Yar gwagwarmayar a Najeriya, Aisha Yesufu, ta bayyana cewa jam’iyyar ADC na ci gaba da firgita wasu ’yan siyasa a ƙasar, yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Aisha Yesufu ta bayyana hakan ne a wani bayani da ta fitar, inda ta ce tasirin da jam’iyyar ADC ke ƙara samu na daga cikin abubuwan da ke haifar da fargaba ga wasu manyan ’yan siyasa da jam’iyyun da suka dade suna jan ragamar mulki.
Ta ƙara da cewa, idan aka yi la’akari da yadda siyasar Najeriya ke sauyawa, akwai yiwuwar a ga fafatawa mai zafi tsakanin jam’iyyun siyasa a zaɓen 2027, musamman idan aka duba yadda jama’a ke ƙara nuna sha’awar sauyi.
Karanta:Mutane 11 sun mutu, gidaje 52 sun kone a sabon rikicin ƙabilanci a Jihar Nasarawa
A cewarta, yanayin da ake ciki na nuna cewa ’yan Najeriya na ƙara fahimtar muhimmancin zaɓe da kuma rawar da za su taka wajen zaɓar shugabanni nagari.
Sai dai ta jaddada cewa dole ne jam’iyyun siyasa su mayar da hankali wajen gabatar da manufofi masu anfani ga al’umma, maimakon dogaro da tsoffin dabarun siyasa.
Recent:An kama ’yan Najeriya uku a India kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
