Daga Mustapha Abdullahi
Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, ya gargadi Nafiu Bala, shugaban wani bangare na jam’iyyar ADC, cewa matakansa na iya kawo illa ga dimokuraɗiyyar Najeriya.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa Kwankwaso, wanda ya koma ADC daga NNPP a watan Maris 2026, ya bayyana haka ne yayin wata hira, inda ya ce ya gayyaci Bala domin sasanta rikicin jam’iyyar amma bai halarci ganawar ba.
Jam’iyyar ADC na fuskantar rikicin shugabanci tun 2025, inda bangarorin Bala da na David Mark ke ikirarin shugabanci, lamarin da ya kai ga kotu da kuma INEC soke amincewa da bangarorin biyu.
Kwankwaso ya bayyana cewa halin da Bala ke ciki na iya cutar da jam’iyyar da kuma dimokuraɗiyya, yana mai kira ga manyan shugabannin al’umma da na addini da su shiga tsakani.
Shi ma Bala ya zargi tsohon shugaban jam’iyyar, Ralph Nwosu, da kakaba shugabanci ba tare da tuntuba ba.
Recent:Matasan Jos North Sun Shirya Zanga-Zangar Lumana Kan Zargin Rashin Adalci.
