Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Wata ’yar kasuwa da ta tsallake rijiya da baya ta ce direba da fasinja ne suka mutu bayan wata mota ɗauke da kayan abin fashewa a hanyar Lumma zuwa Babanna da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja a ranar Lahadi da rana.
Fatima ta ce motar da take ciki tare da wasu ’yan kasuwa da suke dawowa daga kasuwa ba ta da nisa da motar da ta taka bam ɗin.
Ta ce, “Mun je kasuwar Lumma ne lokacin da lamarin ya faru. Motarmu ba ta da nisa da wadda ta taka bam ɗin ba. Tun da farko sojoji sun cire bama-baman da aka binne a hanyar, amma daga baya ’yan ta’adda sun dawo sun sake binne wasu sabbi. Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo mana dauki.”
Fatima ta ƙara da roƙon gwamnati da ta ƙara kaimi wajen kawar da ’yan ta’adda gaba ɗaya daga yankunansu.
Karanta:Join Us For Fair Contest, NDC Tells Aspirants, Gov. Mohammed
Ana zargin cewa ƙungiyar ’yan ta’adda ta Mamudawa ce ta binne bam ɗin, wadda ake ganin tana da alaƙa da ƙungiyar Boko Haram.
Lamarin ya faru ne a daidai wurin da wata gada ta riga ta lalace bayan ’yan sun yi amfani da abin fashewa wajen lalata ta.
Saboda lalacewar gadar ne mazauna yankin suka samar da wata hanyar wucewa a ƙarƙashin gadar domin sauƙaƙa zirga-zirga, musamman ganin cewa yankin na da muhimman harkokin noma da kasuwanci da suka haɗa al’ummomi da dama, ciki har da waɗanda ke iyaka da Jamhuriyar Benin.
Shi ma wani mazaunin yankin, Alhaji Muhammad Sani, ya koka da cewa fiye da manyan ƙauyuka 30 sun rasa hanyar zuwa kasuwanni da sauran wuraren da suke dogaro da su wajen rayuwa.
Ya ce, “Bayan ka bar Wawa idan kana komawa Lumma, akwai manyan al’ummomi sama da 30 masu ɗimbin jama’a da yanzu ba sa iya amfani da wannan hanya gaba ɗaya. Gundumomin siyasa guda huɗu sun fi shan wahala kai tsaye. Akwai Babanna, Kabe/Pissa, Konkoso, Shagunu, Dugga, Wawa da kuma Malale.
Recent:2027: Sen. Buba reaffirms Bauchi governorship Ambition
