Daga Mustapha Abdullahi
Gwamnatin Nasarawa ta musanta rahotannin cewa gwamna Abdullahi Sule ya yi ganawar sirri da Atiku Abubakar a Makka, inda ake ikirarin cewa ya yi alkawarin taimakon kudi domin dakile sake zaben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a 2027.
A cikin wata sanarwa da Ibrahim Addra ya fitar, an bayyana rahoton a matsayin labarin bogi.
Sanarwar ta kara da cewa gwamnan bai taba haduwa da Atiku ko wakilansa ba a lokacin ibadar Umara.
karanta:Advocacy Visit Reveals Gaps In Bauchi Health Facilities, Stakeholders Seek Urgent Action
Gwamnatin ta ce gwamna Sule kullum yana amfani da duk wata dama wajen yabawa shugabancin Tinubu da tabbatar da goyon baya ga gwamnati.
Sanarwar ta ce mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya bayyana cewa bai san irin wannan ganawar ba.
Recent:An fara gangamin tara wa Tinubu magoya baya miliyan 150 -Benjamin Kalu
