Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Wakilan matasa a yankin Jos, ƙarƙashin jagorancin Aliyu Naziru Abubakar, sun sanar da shirin gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Laraba, 8 ga Afrilu, 2026, domin nuna damuwa kan zargin rashin adalci da nuna wariya.
A cewar Aliyu Naziru, ɗaya daga cikin masu shirya zanga-zangar, za a fara taron ne daga Zololo da ke kan titin Bauchi da misalin ƙarfe 8:00 na safe, inda daga nan za a ci gaba da tafiya ta hanyar Bauchi Road.
Karanta;Majalisar dokokin Kano ta jingine tuhumar da take wa tsohon mataimakin gwamna Aminu Abdussalam.
Ya jaddada cewa za a gudanar da zanga-zangar cikin lumana ba tare da tashin hankali ba, tare da kira ga mahalarta da su kiyaye doka da oda a duk tsawon lokacin gudanar da ita.
Ana sa ran samun ƙarin bayani yayin da al’amuran ke ci gaba da wakana.
