Ɗaliban jami’ar Jos, sun bayyana goyon bayan su a kan shirin ƙungiyar malaman jami’oi ta ƙasa, ASUU, na tafiya yajin aiki mako mai zuwa.
Goyon bayan ɗaliban ya biyo bayan wa’adin da ƙungiyar ta ASUU ta bai wa gwamnatin tarayya zuwa nan da ranar 13 ga watan Oktoba a kan ta yi abinda ya dace ko su tafi yajin aikin gargaɗi na makonni biyu.
Shugabar ƙungiyar ɗalibai ta jami’ar Jos, Jane Kanyang Pwajok a madadin ƴan uwanta ɗalibai, ta bayyana cewa goyon bayan ASUU shi ne mafi dacewa da yunƙurin kare ilimi a ƙasar nan.
Ta ce ya zama wajibi duk wani mai sha’awar ganin ci-gaba a fannin ilimi ya goyi bayan manufofin ASUU, inda ta roƙi gwamnatin tarayya da ta gaggauta ɗaukar mataki don tabbatar da cigaban karatu a jami’o’i ba tare da wata katsewa ba
Kiran ɗaliban ya gudana ne a Juma’ar nan, yayin tattaunawa ta musamman tsakanin jagorancin ASUU na jami’ar Jos da wakilan ɗaliban jami’ar.
Tun da fari dai ƙungiyar ASUUn, reshen jami’ar Jos, ta zargi gwamnatin tarayya da gazawa wajen magance matsalolin da suka daɗe suna addabar jami’o’in gwamnati, duk da shekaru na koke-koke da alkawuran da ta ce an yi ba tare da cikawa ba.
Da yake jawabi yayin zaman tattaunawa tsakanin su da ɗaliban da aka gudanar a sakatariyar ƙungiyar da ke Jos, shugaban ƙungiyar reshen jami’ar Jos, Farfesa Jurbe Joseph Molwus, ya bayyana cewa halin da gwamnati ke nuna wa a kan buƙatun ASUU alamu ne na rashin gaskiya da kuma rashin niyya mai kyau.
Ya tunatar da cewa kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) na ASUU kwanan nan ya gudanar da taro a Abuja, inda ya bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwana goma sha huɗu, wanda zai ƙare a ranar 13 ga watan Oktoba domin ta magance buƙatun ƙungiyar ko kuma ASUU ta fantsama yajin aiki na gargadi na makonni biyu.
Cikin bukatun ASUU dai akwai biyan albashin da a ka riƙe a tsarin IPPIS, biyan bashin kuɗaɗen ƙarin girma da alawus na aiki, sakin kuɗin farfaɗo da jami’o’i, da kuma sanya hannu kan yarjejeniyar da a ka sake tsarata ta shekarar 2009 tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU, da sauransu, a cewar Molwus.
Farfesa Molwus ya tunatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a lokacin yaƙin neman zaɓensa na 2022, ya yi alkawarin kawo karshen yajin aikin jami’o’i gaba ɗaya, yana mai cewa, yanzu lokaci ya yi da shugaban zai shiga tsakani kai tsaye don magance matsalolin.
A nashi jawabin, jagoran tattaunawar, Kwamared Jimam Lar, ya bayyana cewa ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi na neman hakkinta yana da matuƙar amfani ga malamai da ɗalibai baki ɗaya.
