Hukumar Kiyaye Hadurra ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar ‘yan jarida bakwai, mambobin Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), a wani mummunan haɗarin mota da ya afku a jihar Gombe. Haka kuma, wasu huɗu sun jikkata a cikin hadarin, kamar yadda aka bayyana a ranar Litinin.

