Majalisar Dattijai ta umurci Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da ya gudanar da bincike kan jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya fadi ko ma ya rasu.
Hukuncin ya biyo bayan korafin da Sanata Titus Zam ya gabatar ƙarƙashin Dokar 42, inda ya nuna damuwa kan yada irin waɗannan jita-jita cikin awanni 48 da suka gabata.
Sanata Zam ya bayyana cewa irin waɗannan labarai suna kawo rudani kuma ba su dace ba, musamman ga Shugaban Majalisar wanda shi ne mutum na uku a ƙasa.
Bayan jefa kuri’a ta murya, an amince da cewa NSA zai binciki tushen da dalilin jita-jitar da ake yadawa kan abin da ake zargin rashin lafiyar Shugaban Majalisar.
Ba wannan ne karon farko ba da ake jita-jitar rashin lafiyar Akpabio, inda a watan Agusta ma aka ta bayyana cewa ya yi rashin lafiya bayan hutun sa a London, amma daga bisani ya musanta hakan kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Zenith Media
