NAJERIYA – Ƙungiyar ƙasashen Turai ta bayyana cikakken goyan bayan ta ga Najeriya sakamakon barazanar kai mata hari da shugaban Amurka Donald Trump ya yi.
Sanarwar da ƙungiyar ta gabatar ya ce suna jajantawa ƴan Najeriya da tashe tashen hankulan da ake samu ya ritsa da su, musamman na baya baya nan da waɗanda aka gani a ƴankin kudancin ƙasar da kuma arewa maso gabas.
Mai magana da yawun sashen kula da harkokin wajen ƙungiyar, Anouar El Anouni ya ce suna sane da kalaman da gwamnatin Amurka ta yi game da Najeriya, kuma suna bayyana cikakken goyan bayan su ga ɗaukacin jama’ar ƙasar da suke fuskantar waɗannan matsaloli na tashin hankali.
Jami’in ya bayyana matsayin ƙungiyar EU na bai wa kowa ƴancin addinin sa ba tare da tsangwama ba, da kuma kare jama’a daga kowanne bangare tare da goyan bayan zaman lafiyar jama’ar ƙasar da yankunan su da kabilunta da kuma addinan su.
EU ta ce tana sane da dalilai da dama dake haifar da tashe tashen hankulan a Najeriya, kuma addini ɗaya ne kawai daga cikin tarin matsalolin dake haifar da irin waɗannan rikice rikice a ƙasar.
Anouni ya ce EU a shirye take wajen ci gaba da haɗin kai da hukumomin Najeriya domin shawo kan matsalolin tsaro.
