Dalibai 50 daga makarantar firamare da sakandare ta St. Mary’s da ke Papiri, Karamar Hukumar Agwara a Jihar Neja, da aka sace, sun samu damar tserewa daga hannun masu garkuwa da su, kuma sun koma hannun iyayensu lafiya.
Rahotanni sun ce daliban sun tsere ne bayan samun damar kubuta daga inda aka kaisu. Ana cigaba da bincike kan yadda lamarin ya faru da kuma kokarin kamo masu laifin.
