A daren nan labari ke zuwa akan cewa Kasar Burkina Faso ta tilastawa jirgin saman sojojin Nigeria saukar gaggawa a kasarta bayan da ta zargi jirgin da shiga kasarta ba bisa ka’ida ba…
Yanzu haka dai jirgin yayi saukar gaggawa a tashar jirage dake garin Bobo-Dioulasso kasar Burkina Faso…
Jirgin yana dauke da sojojin Nigeria guda tara sai matukan jirgin su biyu
Daya daga cikin Jagoran juyin mulki na kasar Burkina Faso ya tabbatar da cewa yanzu haka suna cigaba da bincike akan dalilin da ya sanya jirgin Nigeria ya shiga sararin samaniyar kasarsu ba tare da izini ba…
