Hukumomi a Najeriya sun fara bincike kan kisan wata mata mai suna Fatima Abubakar da ƴaƴanta shida, ɗaya daga cikin kashe-kashe na bayan-bayan nan da ya ja hankalin al’umma, musamman a arewacin Najeriya.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne hukumomi suka ce wasu matasa sun kutsa gidan Malam Bashir Haruna da ke Unguwar Chiranci Ɗorayi da ke birnin Kano tare da yin kisan, lamarin da ya jefa al’ummar jihar cikin alhini.
Tuni shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da lamarin, sannan ya bayyana alhini, tare da kira da a gaggauta gudanar da bincike domin tabbatar da hukunci.
Cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin mummunan rashin imani da rashin tausayi, wanda ya girgiza al’umma da ma ƙasa baki ɗaya kuma ya saɓa wa ƙa’idojin bil’adama.
