Daga shafi na 574 mun tsallaka zuwa shafi na 576 na littafin “From Soldier to Statesman, The Legacy of Muhammadu Buhari” wanda Dakta Omole ya rubuta akan rayuwar tsohon shugaba kasa Muhammadu Buhari. wanda wannnan shafi nuna haƙiƙanin cutar da ta yi ajalin tsohon Shugaban Ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari.
A shafi na 576 an bayyana kai tsaye a littafin, Aisha Buhari ta bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka ƙara tsananta cutar da marigayin ke fama da ita shi ne shan taba sigari da ya yi tun yana da ƙuruciya, tare da cuta ta lumoniya (pneumonia) wadda a ƙarshe ta yi sanadiyyar mutuwarsa.
Ta ƙara da cewa, baya ga hakan, akwai wasu dalilai da suka taru suka ta’azzara lalurar lafiyar marigayin, ciki har da sanyin na’urar sanyaya ɗaki (air conditioner) da ya daɗe yana fuskanta, da kuma shekarun aikin soja, inda suke aiki a cikin ruwa da mawuyacin yanayi, da kuma tsufa, wanda a cewarta duk sun taka rawar gani wajen raunana jikinsa.
